3) Kasar Sin mai tasowa, birnin Beijing mai bunkasuwa
Ran 26 ga watan Mayu, 2009
Birnin Beijing tsohon birni ne mai dimbin tarihi na shekaru aru-aru da suka shude, kuma birnin Beijing cike yake da tsabta tare da bin doka da oda, har yanzu birnin Beijing yana gudanar da zaman rayuwar jama'a cikin wadata, wannan abin ban sha'awa ne kwarai da gaske.
Bisa kallon da na yi wa birnin Beijing , zan iya cewa Sin sansani ce ta masana, tun tsohon karni, Sin tana da shahararrun masana masu fasaha iri daban daban.
Na yi la'akari da yadda fasali ko tsarin gidaje da layuka ko hanyoyi manya da kanana na birnin Beijing, na tabbata cewa, masana tsarin gine-gine na gidaje na kasar Sin tun na tsohon karni har zuwa na yanzu, suna da zurfin ilmi da basira tare da tunani domin na ga suna zuba basira tare da yin wasa da kwakkwalwa wajen fasaha ta tsara gine-gine na gidaje da sauransu. Kamfanoni da masana'antu wadda tsarin yake da kyau da ban sha'awa da kuma ban mamaki ga duk wadda ya shigo kasar Sin.
Fasalin ginin fadar sarakunan gargajiya ta kasar Sin dake birnin Beijing fasali ne tun irin na tsohon zamani, amma har kawo yanzu yana ba wa kowa mamaki da al'ajabi tare da ban sha'awa kwarai da gaske.
Jama'ar kasar Sin kuwa suna ba da cikakken hadin kai da goyon baya ga gwamnatin kasarsu tare da sauran hukumomi daban daban na kasar Sin.
Jama'ar kasar Sin, babba da yaro, suna da kuzari wajen neman abun masarufi, kuma ba su kyamar baki mutanen kasashen ketare, musamman ni bakar fata ko ni na fito daga Afrika.
Jama'ar kasar Sin, babba da yaro, suna mai da hankalisu sosai wajen neman ilmi.
Jama'ar kasar Sin sun samu sauyawa wajen ci gaban zamani, jama'ar kasar Sin ba za su so su yi kama karya ba.
Jama'ar kasar Sin sun sauya ra'ayi na sanya suturarsu ta gargajiya a ko da yaushe, amma ba su daina cin abinci da tsinke ba.
Jama'ar kasar Sin suna da hakuri sosai kuma suna da al'adar son girmama mutane shi ya sa a ko ina aka sadu da juna, za a gai da juna, babu shakka yawan gaisuwa ya fi yawan fada, kuma gaisuwa alama ce ta zaman lafiya a tsakanin al'umma. Jama'ar kasar Sin, babba da yaro, suna da sha'awar motsa jiki. Kasar Sin tana kiyaye hakkin bil adam ko dan adam.