in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata masu fama da ciwon zuciya su sake ganin likita bayan wata guda bayan da aka sallame su daga asibiti
2014-06-16 20:22:13 cri
Wasu masu fama da ciwon zuciya da iyalansu suna tsammanin cewa, bayan da aka sallami masu fama da ciwon daga asibiti, idan suna cikin koshin lafiya, to,shi ke nan sai su huta a gida. Amma masu nazari na kasar Canada sun tunatar da cewa, hakika dai wata guda bayan da aka sallami masu fama da ciwon zuciya daga asibiti yana da matukar muhimmanci gare su. Idan ba su sake ganin likita domin binciken lafiyarsu ba, to, su kan fuskanci babbar barazanar sake kwantawa a asibiti.

Masu nazari daga jami'ar Alberta ta kasar Canada sun bayar da wani rahoto a mujallar ilmin likitanci ta kasar Canada, inda suka bayyana cewa, wata guda na farko bayan da aka sallami masu fama da ciwon zuciya daga asibiti na da matukar muhimmanci gare su. A cikin wannan lokaci mai muhimmanci wato wata guda, idan masu fama da ciwon sun sake ganin likita, barazanar mutuwa ko sake kai su asibiti cikin gaggawa da suke fuskanta ta yi kasa fiye da kashi 10 cikin dari, in an kwatanta su da wadanda ba su sake ganin likita ba. Sa'an nan idan masu fama da ciwon sun ga likitocin da suka san lafiyarsu kwarai da gaske, to, za su kara samun tabbaci wajen kasancewa cikin koshin lafiya.

Masu nazarin sun yi bincike kan masu fama da ciwon zuciya dubu 24 da ke lardin Alberta, wadanda suka taba samun jinya a asibiti. Sakamakon bincikensu ya shaida cewa, masu fama da ciwon da yawansa ya kai kashi 22 cikin dari ba su sake ganin likita ba a cikin wata guda bayan da aka sallame su daga asibiti, yayin da wasu kashi 69 cikin dari sun je ganin likitocin da suka san ciwonsu kwarai da gaske a cikin wata guda bayan da aka sallame su daga asibiti, sa'an nan wasu kashi 9 cikin dari sun je ganin likitocin da ba su san ciwonsu sosai ba. Masu nazarin sun kwatanta halin da wadannan rukunnoni 3 suke ciki, a karshe dai sun gabatar da shawarar da aka ambaya a baya.

Masu nazarin sun ce, ko da yake bayan da aka sallami masu fama da ciwon zuciya daga asibiti, likitoci su kan yi amfani da wani tsarin musamman na kintace domin tunatar da masu fama da ciwon su dauki matakan rigakafin sake barkewar ciwon, amma ta hanyar amfani da wannan tsari su kan tabbatar da masu fama da ciwon da suke fuskantar babbar barazana da yawansu ya kai kashi 60 cikin dari kawai. Don haka ya kamata masu fama da ciwon zuciya su tuntubi likitocinsu yadda ya kamata bisa halin da suke ciki.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China