in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rintsawa da rana na taimakawa wajen kyautata kwarewar mutum ta haddacewa da karatu
2014-04-07 16:37:51 cri
A kwanan baya, wasu masu nazari na kasar Japan sun kaddamar da wani sabon sakamakon nazari da ke cewa, baya ga tabbatar da isasshen lokacin yin barci da dare, rintsawa da rana na iya taimakawa wajen kyautata kwarewar mutum ta haddace abubuwa a kwakwalwa da karatu.

Wasu masu nazari daga jami'ar Waseda ta kasar Japan sun yi gwaje-gwaje kan mutane 16, wadanda aka raba su zuwa rukunoni 2, tare da koya musu yadda ake jefa kananan kwallaye daya bayan daya zuwa sama sa'an nan a cafe su. Bayan wadannan mutane 16 sun yi mintoci 30 suna gwada hakan, an bukaci 'yan rukunin farko su yi barci na mintoci 70, 'yan daya rukunin kuma su yi kallon talibijin ko karanta littattafai.

An gano cewa, bayan yin barci na tsawon mintoci 70, 'yan wannan rukuni sun samu saurin ci-gaba. Kafin barcin, ko wanensu kan kama kwallayen sau 4 kawai. Amma bayan barcin, adadin ya karu zuwa kusan 8. A hannu guda kuma, wadanda suka yi kallon talibijin ko karanta littattafai a maimakon yin barci ba su samu ci-gaba sosai ba, sun kama kwallayen kusan sau 5 a maimakon kusan 4 a baya.

Kashegari, masu nazarin sun ci gaba da yin gwaje-gwaje kan kwarewarsu ta kama kwallayen, inda suka gano cewa, wadanda suka rintsa da rana sun gwanance wajen kama kwallayen cikin saurin gaske, inda su kan kama kwallayen kusan sau 15, yayin da wasu wadanda aka ware su 8 da ba su rintsa da rana ba suka kama kwallayen kusan sau 8 kawai. A bayyane bambancin da ke tsakanin rukunonin 2 ya ci gaba da karuwa.

Masu nazarin suna ganin cewa, rintsawa ba kawai na iya kyautata kwarewar mutane ta motsa jiki ba ne, har ma na iya kyautata kwarewarsu ta fannin karatu. Idan wani mutum ya koyi abubuwa a farke, a kan adana wadannan abubuwa a wani sashen tsakiyar kwakwalwarsa a cikin gajeren lokaci, kuma a yayin da yake barci, a kan daidaita wadannan abubuwa, a kan kai su sassa daban daban na kwakwalwarsa, inda za a adana su a matsayin abubuwan da ba zai iya mantawa ba.

Saboda haka, masu nazarin sun bai wa wadanda suke namijin kokarin cin jarrabawa ko kuma 'yan wasan da ke samun horo wata shawarar da ke cewa, idan sun karbi bayanai da yawa fiye da yadda kwakwalwarsu ke iya daidaitawa a rana, watakila yin barci da dare ba zai isshe su ba. Rintsawa da rana na iya taimakawa kwakwalwarsu wajen rarraba da daidaita bayanai, ta yadda za su iya samun sakamako mai kyau.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China