in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila cin abinci mai yawan maiko da sukari a lokacin da wata mace take da juna biyu zai iya sanya 'ya'yanta su sha giya har su wuce gona da iri
2014-04-14 14:49:08 cri
Kamar yadda kowa ya sani, wasu kungiyoyi a fannin ilmin likitanci da kuma likitoci sun yanke shawarar cewa, masu juna biyu kada su ci abinci mai yawan maiko da sukari. Wannan shawara ta biyo bayan gwaje-gwajen da aka yi kan dabbobi a kwanan baya sun nuna cewa, lokacin da wata mace take da juna biyu, ta kan ci abinci mai yawan maiko da sukari fiye da yadda ya dace, to, idan ta yi hakan, zai haddasa 'ya'yanta ba kawai su yi fama da matsalar samun kiba ba, har ma su kara fuskantar barazanar shan giya fiye da kima ko magani fiye da yadda suke bukata.

Kwararru a bangaren ilmin likitanci daga jami'ar Florida ta kasar Amurka da ke gudanar da wannan nazari sun nuna cewa, a halin yanzu a ko ina ake iya sayen kayayyakin abinci masu dandano wadanda cike suke da mai da sukari. Watakila nauyin yawancin masu juna biyu na Amurka ya wuce yadda ya kamata ne sakamakon cin irin wadannan kayayyakin abinci fiye da kima. A wani hannu na daban kuma, yawan yara masu kiba na ta karuwa, sa'an nan yawan matasan da suka wuce gona da iri wajen shan giya da magunguna sai kara karuwa yake a halin da ake ciki yanzu. Ya kamata daga tushe ne a yi nazari kan wadannan matsalolin da suka kara damun mutane.

Masu nazarin sun ciyar da wasu beraye mata da abinci mai yawan mai, yayin da suka ciyar da wasu na daban da abinci mai yawan sukari. Sun gano cewa, in an kwatanta 'ya'yan beraye mata wadanda aka ciyar da su yadda ya kamata, 'ya'yan beraye mata da aka ciyar da su da abinci mai yawan maiko su kan rungumi al'adar shan giya bayan da suka yi girma, kana yawan wani nau'in sinadarin da ya kan haddasa ciwon zuciya ya yi yawa a jikinsu. 'Ya'yan beraye mata da aka ciyar da su da abinci mai yawan sukari su ma haka, wadanda kuma su kan kamu da shan miyagun kwayoyi bayan da suka yi girma. Bayan haka kuma, nauyin 'ya'yan beraye mata da aka ciyar da su da abinci mai yawan mai da sukari ya fi yawa.

Wannan nazari ya tabbatar da sakamakon nazarin da aka yi kan dabbobi a baya, wato cin abinci da yawa fiye da kima na iya sauya yadda kwakwalwa take aiki. Idan wani ya kan ci kayayyakin abinci masu yawan mai da sukari, ya kan fito da wani nau'in alamar da ta kusan yi daidai da yadda aka sha miyagun kwayoyi. Masu nazarin na Amurka sun nuna cewa, ko da kananan beraye suna cikin cikin mahaifansu mata, kayayyakin abinci masu yawan mai da sukari su kan kara nauyin kananan berayen, tare da kara jarabarsu kan giya da magani.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China