in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gagarumin matsin lambar da ake fuskanta a ayyuka na kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya
2014-05-12 15:53:43 cri

A zamanin yanzu, kullum mutane kan fuskanci gagarumin matsin lamba sakamakon ayyukansu. Wani sabon nazarin da aka yi a kasashen Turai ya nuna mana cewa, mutanen da suka fuskantar babban matsin lamba a ayyukansu suna kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon zuciya, don haka idan mutane ba su fito da wata hikimar sassauta matsin lambar da suke fuskanta a ayyukansu ba, to, fa, ba za su iya kyautata lafiyarsu ba.

Shahararriyar mujallar ilimin likitanci ta kasar Birtaniya mai suna "wukar likita" wato The Lancet ta wallafi wani bayani a kwanan baya da ke nuna cewa, wata kungiyar nazari ta kasa da kasa ta gudanar da bincike kan bayanan da suka shafi lafiyar mutane kusan dubu 200 da ke zaune a kasashen Belgium, Denmark, Finland, Faransa, Holland, Sweden da Birtaniya. Sun gano cewa, barazanar kamuwa da ciwon zuciya da mutanen da suke fi daidaita babban matsin lamba a ayyukansu suke fuskanta ta fi sauran mutane yawa har da kashi 23 cikin dari. Dalilin da ya sa suke gamuwa da gagarumin matsin lamba a ayyuka shi ne domin akwai bukatu da dama da dole ne su biya yayin da suke gudanar da ayyukansu, kuma ba su ba da jagora a kan ayyukansu ba.

Masana ilmin likitanci da suka gudanar da nazarin, sun fito ne daga jami'ar London ta kasar Birtaniya sun bayyana cewa, sakamakon nazarinsu ya tabbatar da cewa, akwai alaka a tsakanin matsin lamba ta fuskar ayyuka da kuma barazanar kamuwa da ciwon zuciya. Ko da an yi la'akari da halin da mutanen da aka yi musu bincike suke kasancewa, alal misali, shekarunsu a duniya, jinsinsu, kudin shigarsu, hanyar zaman rayuwarsu da dai makamantansu. Haka zalika an sake kidaya da bincike, duk da haka akwai irin wannan alaka. Saboda haka idan an yi dabarar rage matsin lamba ta fuskar aiki, to, hakan zai taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya.

Wasu kwararru sun nuna cewa, matsin lamba ta fuskar aiki da aka ambata a wannan nazari, wani nau'in illa ne da yanayin aiki yake kawo wa tunanin mutane kawai. Mai yiwuwa ne mutane su fuskanci matsaloli daban daban, alal misali, fargabar ko za a sallame su daga wuraren ayyukansu? Don haka watakila barazanar kamuwa da ciwon zuciya da mutane suka fuskanta sakamakon matsin lamba ta fuskar aiki a hakikanin zaman rayuwarsu za ta fi yadda sakamakon nazarin ya nuna tsanani. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China