in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shayar da jarirai da nonon uwa na iya rage barazanar yaduwar kwayoyin cutar Sida ta AIDS a tsakanin jarirai da mahaifansu mata
2014-05-06 16:09:18 cri
Sakamakon wani sabon nazari ya nuna mana cewa, idan mahaifa mata wadanda suka kamu da cutar Sida ta AIDS sun dade suna shayar da jariransu da nononsu, to, yawan kwayoyin cutar ta Sida da ke cikin nononsu zai ragu, kuma watakila hakan zai rage wa jariran barazanar kamuwa da cutar.

A yawancin lokaci, yawan yiwuwar kamuwa da cutar ta Sida ta hanyar nonon mahaifa mata da jarirai suke fuskanta ya kai kasha 10 zuwa 15 cikin dari. Masu nazari daga kwalejin ilimin kiwon lafiyar al'umma na Mailman da ke jami'ar Columbia ta kasar Amurka sun yi shekaru 2 suna gudanar da wani nazari kan darurruwan matan kasar Zambiya da suke fama da cutar ta Sida da kuma jariransu, a kokarin tabbatar da cewa, ko bambancin lokacin shayar da jarirai da nonon uwa da sauran sauye-sauye za su ba da tasiri kan raguwar yawan kwayoyin cutar Sida da ke cikin nonon uwan.

Da farko dai masu nazarin sun bai wa dukkan mahaifan mata shawarar shayar da jariransu da nononsu a kalla watanni 4 bayan da suka haife su, kuma bayan watanni 4, rabin mahaifan sun daina shayar da jariransu da nononsu, rabin na daban kuma sun ci gaba da yadda suka yi a cikin watannin 4. Bayan da masu nazarin suka kwatanta sakamakon binciken, sun gano cewa, a cikin mahaifan mata wadanda suka dade suna shayar da jariransu da nononsu, yiwuwar kasancewar kwayoyin cutar Sida da ke cikin nononsu ba ta kai kashi 40 cikin dari ba, kana kuma yawan kwayoyin cutar da ke cikin nononsu ya ragu. Amma a cikin wadanda suka daina shayar da jariransu da nononsu kuwa, yiwuwar kasancewar kwayoyin cutar Sida da ke cikin nononsu ta kai kashi 80 cikin dari ba, kana kuma yawan kwayoyin cutar da ke cikin nononsu ya yi yawa in an kwatanta su da wadanda suka dade suna shayar da jariransu da nononsu.

An kaddamar da wannan sakamakon nazari kan shafin intanat na wata mujallar Amurka mai suna "sauya kimiyya zuwa ilmin likitanci" wato Science Translational Medicine. Masu nazarin sun bayyana cewa, sakamakon nazarin nasu ya nuna cewa, tsawaita lokacin shayar da jarirai da nonon uwa yana iya rage yawan kwayoyin cutar ta Sida da ke cikin nonon uwan. Nazarin yana da babbar ma'ana wajen rage barazanar yaduwar cutar Sida a tsakanin jarirai da mahaifansu mata.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China