in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinadarin DHA na iya kyautata kwarewar yara ta karantawa
2014-05-27 08:30:43 cri
Wasu masu nazarin kimiyyar kasar Birtaniya sun furta a kwanan baya cewa, bai wa yaran da ba su kware wajen karanta littattafai ko bayanai ba sinadarin DHA yana iya kyautata kwarewarsu ta karatu, sa'an nan kuma yana taimakawa wajen sassauta fitinar da su kan yi a zaman yau da kullum.

Masu nazari daga jami'ar Oxford ta Birtaniya sun kaddamar da rahoton nasu ne a kwanan baya, inda suka nuna cewa, sakamakon yin hadin gwiwa da wasu makarantun firamare da ke yankin Oxford, ya sa suka gayyaci yara fiye da 360 da shekarunsu ba su wuce 7 zuwa 9 ba a duniya domin shiga gwaje-gwajen nasu. A cikin makonni 16, wasu daga cikin wadannan yara sun sha sinadarin DHA da yawansu ya kai miligiram dari 6 a ko wace rana, yayin da sauran kuma suka sha wasu abubuwan da ba su da amfani ko kadan, daga baya an gwada su tare.

Sakamakon gwajin ya shaida cewa, idan yaran da ba sa samu maki mai kyau a jarrabawar karanta bayanai suka sha sinadarin na DHA, to, kwarewarsu ta karatu kan kyautatu sosai. Bayan da aka kammala gwaje-gwajen, yara wadanda a da a baya suke a cikin azuzuwansu a fannin karatu, kwarewarsu ta karatu ta kyautata sosai fiye da yadda aka zata.

Ban da haka kuma, a cikin rahotannin da iyayen yaran suka rubuta, an ce, yaran da suka sha sinadarin DHA ba su fiye fitina kamar yadda suke yi a baya ba.

Masu nazarin sun bayyana cewa, a baya, sakamakon wasu nazari ya shaida cewa, shan sinadarin na DHA na iya taimakawa yaran da suke fama da matsalar karatu da kuma masu fama da cutar dake haifar da rashin natsuwa. Yaran da aka yi musu bincike a wannan karo, yara ne da suke cikin koshin lafiya, ko da yake wasu daga cikinsu ba su samu maki mai kyau a jarrabawar karatu ba, amma sun rabu da wadancan cututtuka. Ta haka ma iya cewa, shan sinadarin na DHA na iya taimakawa dukkan yara baki daya.

Ana dai yawan tabo batu kan wannan sinadarin na DHA. A baya, sakamakon nazari ya shaida cewa, sinadarin DHA da dangoginsa suna taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini da dai makamantansu.

Masu sauraro, za ku iya samun yawan wannan sinadarin na DHA a cikin kifaye iri daban daban da kuma sauran dabbobin ruwa.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China