in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar na son kara hadin gwiwa da kasar Sin kan aikin nazarin kayayyakin tarihi
2019-03-04 10:58:24 cri

Kasar Masar na neman kara hadin gwiwa da kasar Sin, kan harkokin da suka shafi nazarin kayayyakin tarihi, bayan aikin da wani shiri na kasar Sin ya yi karo na farko a Masar a 2018.

A cewar Ministan kula da kayayyakin tarihi na Masar, Khaled al-Anany, shiri kan nazarin kayayyakin tarihi da kasar Sin ta yi karon farko a Masar a bara, ya yi amfani, inda yake fatan shi ne mafari ga irin ayyukan da kasar za ta yi a Masar.

Ministan na nufin shirin kasar Sin na cibiyar kula da harkokin nazarin kayayyakin tarihi ta kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa, wanda ya fara aiki cikin watan Nuwamban bara, a wurin bautar Montu dake arewacin harabar fitaccen wurin ibada na Karnak dake lardin Luxor na Masar.

Khaled al-Anany, ya ce shirin na kasar Sin ya kammala aikinsa na farko a Masar, wanda galibi ayyuka ne na sharar fage.

Ya kara da cewa, a nan gaba, ana sa ran jami'an kasar Sin da takwarorinsu na Masar, za su fara tattarawa da sake harhada ayyuka da wasu kayayyakin Montu da suke a warwatse.

Ministan kuwa ya bayyana fatansa na ganin yadda za su samu nasara a fannin nazarin kayayyakin tarihi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China