Ranar 7 ga wata ne, wasu masu tsattsauran ra'ayi suka kai hari a wajen binciken ababan hawa na sojoji dake garin Rafah a arewacin Sinai a kasar Masar, inda mutane gomai suka rasa rayukansu ko suka jikkata.
Dangane da lamarin, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yi tir da wannan harin ta'addanci, kana tana adawa da duk wani nau'i na ta'addanci, tana kuma goyon bayan kokarin kasar Masar na yaki da 'yan ta'adda, da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar. (Tasallah Yuan)