in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Jiarui ya gana da shugaban kasar Masar
2016-12-02 10:13:19 cri

Jiya Alhamis ranar 1 ga wata bisa agogon wurin, Wang Jiarui, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi a Alkahira, babban birnin kasar, yayin da yake ziyara a Masar tare da tawagar Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

A yayin ganawar, Wang Jiarui ya bayyana cewa, kasar Sin na mara wa kasar Masar baya da kokarin da take yi don samun zaman karko da ci gabanta. Kasar Sin na da aniyar yin hadin gwiwa tare da Masar wajen aiwatar da muhimman ra'ayoyi bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara tattaunawa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare domin neman samun bunkasuwa, da inganta hadin kansu da cudanyarsu a fannoni daban daban, a kokarin ciyar da dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu zuwa gaba daga dukkan fannoni. Bayan hakan, Wang Jiarui ya yi bayani kan halin da kasar Sin ke ciki wajen tattalin arziki da zamantakewar al'umma, gami da muhimman ra'ayoyin da aka cimma a cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiya na 18 na JKS.

A nasa bangaren kuma, shugaba Sisi ya bayyana cewa, kasarsa na mai da hankali kan kasar Sin, da dora muhimmanci kan yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Masar tana kuma goyon bayan shirin "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, da maraba da zuwan kamfanonin Sin wajen kara zuba jari a Masar, domin ba da taimako wajen ci gaban tattalin arzikin Masar. Bugu da kari, Shugaba Sisi ya yi bayani kan halin da Masar ke ciki a fannonin siyasa da tattalin arziki, tare da bayyana ra'ayoyinsa kan wasu lamuran shiyya-shiyya da na kasashen duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China