in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Masar
2017-04-25 10:52:07 cri

Jiya Litinin ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Masar Sameh Shoukry, a yayin taron farkon ministoci, na dandalin tattaunawa tsakanin kasashe masu dadadden tarihi a birnin Athens.

Yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da ya faru a kasar Masar kwanan baya. Ya ce Masar muhimmiyar abokiya ce ta kasar Sin wajen raya shirin "Ziri daya da hanya daya", kuma Sin na maraba da Masar wajen halartar taron koli na kasashen da shirin ya shafa, wanda zai gudana a wata mai zuwa, inda bangarorin biyu za su tattauna kan manufofinsu na raya kasa, da kara azama ga cimma moriyar juna da samun nasara tare. Kaza lika ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye mu'amala da Masar a cikin harkokin kasashen duniya.

A nasa bangaren kuma Mr. Shoukry ya nuna cewa, dangantakar da ke tsakanin Masar da Sin, wani muhimmin bangare ne na manufofin diplomasiyyar kasar sa. Kuma kasashen biyu suna da matsayi kusan iri daya game da harkokin kasashen duniya, yayin da a hannu guda suke raya mu'ammala tsakaninsu yadda ya kamata. Mr. Shoukry ya ce, kasar sa za ta aiwatar da ra'ayoyi na bai daya, wadanda shugabannin kasashen biyu suka cimma, da inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare, gami da sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannoni daban daban. Bugu da kari, Masar na da aniyar neman wata sabuwar hanyar hadin kai bisa inuwar shirin "Ziri daya da hanyar daya".(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China