in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da aikin gina yankin cinikayya na tsakiya na sabon babban birnin kasar Masar
2018-03-19 12:33:16 cri

An kaddamar da aikin gina yankin cinikayya na tsakiya na sabon babban birnin kasar Masar jiya Lahadi bisa agogon wurin. Firaministan kasar Masar Sherif Ismail da ministocin kasar da dama, da jakadan kasar Sin da ke kasar Song Aiguo da mataimakin shugaban kamfanin gina gine-gine na kasar Sin Zheng Xuexuan na daga cikin wadanda suka halarci bikin tare da gabatar da jawabai.

A cikin jawabinsa, Mr. Sherif Ismail ya furta cewa, aikin gina yankin cinikayya na tsakiya na sabon babban birnin kasar Masar zai samar da guraban aikin yi fiye da 1000 ga 'yan kasarsa, haka kuma kafuwar yankin za ta kyautata muhallin zaman 'yan kasar sosai.

A matsayinsa na wanda ke bangaren kula da aikin ginin, Mr. Zheng Xuexuan ya bayyana cewa, gudanar da aikin yadda ya kamata zai saukakawa yawan mazauna birnin Alkahira da ma cunkoson zirga-zirgar birnin, da kuma samar da wani kyakkyawan muhallin jawo jari, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasar zirin tattalin arziki na kogin Suez na kasar da zirin tattalin arziki na Bahar Maliya, a kokarin taimakawa cimma burin farfado da kasar Masar. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China