in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin yada al'adun yankin yammacin kasar Sin a Masar
2017-07-07 11:16:36 cri
A jiya Alhamis da dare ne, a cibiyar fasaha ta El Hanager dake Alkahira, babban birnin kasar Masar aka bude bikin "Yada al'adun yankin yammacin kasar Sin na shekarar 2017", mai taken al'adun jihar Xinjiang ta kasar Sin.

A sakon da ya aike yayin bikin, zaunannen wakilin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya ta Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, Yu Zhengsheng, wanda mataimakiyar ministan harkokin fadakar da jama'a, kana mataimakiyar shugaban ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin Cui Yuying ta wakilce shi ya ce, kasar Masar ita ce kasa ta farko da ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin a duk fadin nahiyar Afirka, ya zuwa yanzu, ko da shekaru sama da 60 suka wuce, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na ci gaba da bunkasuwa cikin yanayi mai kyau.

A nan gaba, shawarar ziri daya da hanya daya za ta ci gaba da samar wa kasashen biyu sabbin damammaki game da raya dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin har da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Masar Mahmoud El-Sharif, tsohon firaministan kasar Essam Sharaf, da kuma jakadan kasar Sin dake kasar Masar Song Aiguo daga bisani suka gabatar da jawabai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China