in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron JKS na 19 zai samar da sabbin damammaki ga Sin da Masar wajen raya dangantakar dake tsakaninsu
2017-11-29 10:49:10 cri
A jiya Talata, jakadan kasar Sin dake kasar Masar Song Aiguo, ya bayyana a yayin taron karawa juna sani mai taken "dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Masar a halin yanzu da kuma nan gaba" cewa, gudanarwar taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 19, ta samar da sabbin damammaki masu kyau ga kasar Sin da kasar Masar wajen raya dangantakar dake tsakaninsu, kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zai samu bunkasuwa ya zuwa wani sabon matsayi.

Haka kuma, ya ce, a yayin taron wakilan JKS karo na 19, an tabbatar da manufar gina sabuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasashen ketare bisa ka'idojin nuna girmamawa ga juna, da kiyaye yanayin adalci da kuma bunkasa hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, wannan shi ne babban burin kasar Sin a fannin raya harkokin diflomasiyya.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Masar, tun lokacin da aka kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu a shekarar 2014, an samu ci gaba sosai bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da siyasa.

A nan gaba kuma, kasar Sin tana fatan kara mu'amala tsakaninta da kasar Masar kan harkokin neman bunkasuwa da kuma yin hadin gwiwa, domin cimma moriyar juna da kuma samun ci gaba tare.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar da cibiyar ba da shawara ga majalisar ministoci ta kasar Masar sun shirya taron ne cikin hadin gwiwa, inda masana kimanin 150 daga jami'ar Peking, da jami'ar Alkahira, da hukumomin da abun ya shafa sun halarci wannan taro.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China