in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin ya gana da mukaddashin shugaban kwamitin AU
2018-05-13 16:12:14 cri
A ranar 11 ga wata, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Zhanshu, wanda yake ziyarar aiki a kasar Habasha, ya gana da mukaddashin shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Thomas Kwesi Quartey a birnin Addis Ababa, yayin da ya kai ziyara a hedkwatar kungiyar ta AU.

A yayin ganawar tasu, Li Zhanshu ya bayyana cewa, a watan Satumba na shekarar bana, za a gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar tsakanin kasashen Sin da Afirka, inda shugabannin kasashen Sin da Afirka za su tattauna, kan yadda za a habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu cikin sabon zamani, da yadda za a cimma moriyar juna da kuma neman ci gaba tare. Kuma ana da imanin cewa, taron na wannan karo zai kasance mai muhimmanci, zai kuma karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka, yayin da ake ciyar da bunkasuwar Sin da Afirka gaba bisa kyakkyawan hadin gwiwar dake tsakanin sassan.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta dukufa wajen nuna goyon baya ga kungiyar AU a fannonin gina hukumominta, da kyautata ayyukan kiyaye zaman lafiya, da kuma gina ababen more rayuwa. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana goyon bayan kungiyar, wajen jagorantar aikin dunkulewar kasashen Afirka baki daya, da kuma samar da karin tasiri kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, domin kare hadin kan kasashen Afirka, da kuma moriyar su.

A nasa bangare kuwa, Mr. Quartey ya yi maraba da ziyarar Li Zhanshu a babban ginin helkwatar kungiyar AU, ginin da ke alamta kyakkyawan hadin gwiwar Sin da Afirka. Ya kuma godewa kasar Sin, dangane da babban taimakon da ta baiwa kungiyar. Ya ce, kungiyar AU tana sa ran halartar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wanda za a yi a birnin Beijing, yana kuma fatan za a zurfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyar AU da kasar Sin yadda ya kamata, kuma bisa dukkan fannoni, ta yadda kungiyar za ta sami karin taimako daga bangaren Sin a fannonin gina ababen more rayuwa, da ba da ilmi, da kuma raya harkokin kimiyya da fasaha da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China