in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun sha alwashin ci gaba da yaki da rashawa da almundahanar kudi
2018-04-18 11:05:06 cri
Ministoci daga kasashen Afrika sun nanata aniyarsu na cigaba da yakar ayyukan rashawa da zambar kudade a yayin da suka yi wani taro a babban birnin kasar Habasha.

Taron na kwanaki 6 wanda shi ne karo na biyu na taron shekara shekara na kwamitin kwararru kan harkokin kudi da tsare tsaren tattalin arziki da raya ci gaba na kungiyar tarayar Afrika (AU), wanda aka kammala shi a ranar Talata, a helkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa.

Jami'an na kasashen Afrika sun gabatar da bukatar karfafa matakan yaki da rashawa da zambar kudade a fadin nahiyar.

A jawabin da ta gabatar a yayin taron ministocin, kwamishinar AU mai kula da walwalar jama'a Amira El Fadil ta ce, rashawa ita ce babbar matsalar dake dakile ci gaban nahiyar Afrika.

Kungiyar tarayyar Afrika ta ayyana batun yaki da rashawa a matsayin babban jigon taronta na shekarar nan ta 2018.

Haka zalika taron ministocin ya kuma bayyana bukatar jajurcewa wajen yakar laifuffukan da suka shafi almundahanar kudade da halasta kudaden haram a nahiyar ta Afrika, wanda yake haifar da hasarar dala biliyan 50 ga nahiyar a duk shekara.

A cewar Fadil, kungiyar AU tana cigaba da yin aiki tare da sauran hukumomi domin bankado dukkan kudaden da aka karkatar da su ta barauniyar hanya daga kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China