in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta tallafawa kasashen Afrika wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi
2018-04-12 10:26:19 cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta sha alwashin tallafawa kasashen nahiyar Afrika wajen tattara kudaden da za'a yi amfani da su na magance matsalar sauyin yanayi ta hanyar alkawurran da aka dauka na taimakon gudunmowar da kasashen za su bayar wato (NDCs) a takaice.

Josefa Sacko, kwamishiniya mai kula da raya karkara da aikin gona ta kungiyar AU, ta ce, kungiyar za ta sanya ido domin tabbatar da ganin dukkan kasashen sun tsaya tsayin daka domin ganin an cimma burin da aka sanya gaba.

Sacko ta fada a lokacin taron dandalin Africa Carbon Forum karo na 10 a Nairobi cewa, nasarar alkawurran da aka dauka, shi ne zai tabbatar da irin matakan da aka aiwatar na tunkarar matsalolin sauyin yanayi bayan shekarar 2020.

Ta bayyana cewa, baya ga yin aiki tare da masu shiga tsakani game da matsalar sauyin yanayi na Afrika, kungiyar AU tana kokarin samar da kwararru domin tallafawa gwamnatocin Afrikan.

Bugu da kari, Richard Munang, jami'in MDD mai kula da muhalli da sauyin yanayi a Afrika ya ce, za'a iya dora alhakin matsalolin sauyin yanayi bisa ga salon rayuwa da wasu mazauna karkara a sassan nahiyar ke gudanarwa.

Munang ya fadawa wakilai mahalarta taron dandalin cewa, matsalolin da suka hada da karancin abinci mai gina jiki da rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, suna cigaba da ta'azzara don haka ya bukaci a hanzarta daukar matakan takawa matsalolin birki karkashin shirin raya kasashen nahiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China