in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bayyana sauyin shugabanci a Habasha da cewa muhimmin al'amari ne
2018-04-04 10:10:27 cri
Shugaban kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya yaba da yadda aka mika mulki a Habasha cikin kwanciyar hankali inda ya bayyana cewa ya kasance wani muhimmin batu ne ga kasar ta gabashin Afrika har ma da nahiyar Afrika baki daya.

Mahamat ya yi wannan tsokaci ne a lokacin ganawa da sabon firaiministan kasar Habasha, Abiy Ahmed.

Ganawar ta Ahmed da Mahamat ita ce ta farko a hukumance, tun bayan da sabon firaiministan ya kama aiki a ranar Litinin bayan da ya karbi aiki daga hannun tsahon firaiministan kasar Habashan Hailemariam Desalegn, wanda ya yi murabus daga aiki a ranar 15 ga watan Fabrairu sakamakon zanga zangar kin jinin gwamnatin da aka gudanar a sassan kasar.

Mahamat ya yabawa kokarin gwamnatin Habasha bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da batutuwan da suka shafi cigaban shiyyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China