Cikin wata sanarwa da AU ta fitar ta nuna cewa, cibiyoyin uku da za'a kafa a Yaounde sun hada da cibiyar nazarin sha'anin mulki da kimiyyar yanayin zamantakewar al'umma ta jami'ar Pan African(PAU), da asusun bada lamini na Afrika wato African Monetary Fund (AMF); da kuma majalisar harkokin wasanni ta Afrika.
Sarah Anyang Agbor, kwamishiniya mai kula da sashen ma'aikata, kimiyya da fasaha (HRST) ta AU, da Lejeune Mbella Mbella, ministan harkokin wajen jamhuriyar Kamaru ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin bangarorin biyu a ranar Juma'a.
Sanarwar tace an kwashe sama da shekaru 10 ana tattaunawa gabanin an cimma matsayar kafa cibiyoyin na AU uku, kana an shafe shekaru 5 ana cimma daidaito kafin a gama daddalewar karshe na kafa cibiyoyin.
Kwamishiniyar tace, sanya hannu kan yarjejeniyar ya kasance mai matukar muhimmanci kasancewa an gudanar dashi ne 'yan kwanaki kadan bayan da aka amince da yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci tsakanin kasashen Afrika wato (AfCFTA).