Shugaban wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da yake tattaunawa da shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya a birnin Nairobin kasar Kenya, ya yaba da kokarin Kenya na samar da zaman lafiya a shiyyar kana ya yi kira ga kasashen dake shiyyar, da su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta kudun.
Mahamat ya kuma yi kira ga shugaba Kenyatta da takwarorinsu na gabashin Afirka da su ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan ta kudu. (Ibrahim Yaya)