Yayin da yake ganawa da shugaba Teshome, Li Zhanshu ya isar masa da gaisuwa daga shugaban kasar Sin Xi Jinping. Ya ce, wannan ne karo na farko da ya kai ziyara kasar waje tun bayan da ya zama shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wannan ya shaida cewa Sin ta dora muhimmanci ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Habasha da kuma nahiyar Afirka. Sin tana son hada kai tare da kasar Habasha wajen inganta hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, shugaba Teshome ya nuna godiya ga kasar Sin bisa ga goyon bayan da ta dade tana nunawa kasar Habasha. A yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, kasar Habasha tana son hada kai tare da kasar Sin wajen inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. (Zainab)