Ga Mutanen Da Aka Nuna Musu Yabo:
Ma Shanxiang
Sana'a: Mai shiga-tsakani kan harkokin jama'a na titin Guanyinqiao dake unguwar Jiangbei ta birnin Chongqing
Labari: A kan kira shi da sunan "Lao Ma", kamar dattijo Ma, wanda ya gudanar da aikin shiga-tsakani har na tsawon shekaru 29, ya cimma nasarar aikin shiga-tsakani kan harkokin jama'a fiye da dubu 2.
Shugaba Xi Jinping ya ce, ana bukatar jami'ai kamar Lao Ma da su taka muhimmiyar rawa a matsayin dan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da bin tunanin kwamitin tsakiya na jam'iyyar, da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.