Yana ganin cewa, a halin yanzu, ya dace a gudanar da jagoranci cikin hadin gwiwa, kana kasar Amurka tana son nuna karfinta wajen yin jagoranci ta hanyar bin manufofin nuna kiyaya, lamarin da ya bata ran kasa da kasa kwarai da gaske.
A yayin taron nemama labarai da aka yi a hedkwatar MDD dake birnin New York, Mr. Lavrov ya bayyana cewa, a karkashin jagoranci na Donald Trump, tasirin kasar kan wasu muhimman batutuwan kasa da kasa yana ci gaba da raguwa, manufofin diflomasiyya na kasar sun yi matukar canzawa idan aka kwatanta da na baya, misali kasar Amurka ta fita daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris da kuma yarjejeniyar kasa da kasa kan batun 'yan gudun hijira da UNESCO ta tsara.
Bugu da kari, Mr. Lavrov yana zargin kasar Amurka cewar, ta rage taimakonta ga wasu kasashen duniya da kuma gudummawar da ya kamata ta baiwa MDD. (Maryam)