in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Rasha da Amurka sun yi shawarwari kan batun yaki da ta'addanci a Syria
2016-06-14 10:43:15 cri
A jiya Litinin, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Amurka John Kerry kan yadda za su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu wajen yaki da 'yan ta'adda a kasar Syria, da kuma warware rikicin kasar Ukraine da dai sauransu.

Mr. Lavrov ya jaddada cewa, ya kamata a bambanta kungiyoyi masu adawa da gwamnatin kasar Syria wadanda suke nuna amincewa da kasar Amurka da kungiyoyi masu sassaucin ra'ayi, a hali kuma wadannan kungiyoyi masu sassaucin ra'ayi su ne masu aikata laifuffukan ta'addanci.

Kaza lika, ministocin biyu sun jaddada cewa, ba za su baiwa 'yan ta'addan kasar Syria dama ba wajen shigar da kayayyakin da suke bukata daga yankin iyakar dake tsakanin Syria da Turkiya.

Daga bisani kuma, sun tattauna kan yadda za a warware rikicin Ukraine da wasu batutuwan dake shafar kasa da kasa da kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China