in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Amurka da Rasha za su tattauna kan batun Ukraine da Syria a birnin Washington
2017-05-09 11:17:36 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson da takwaransa na Rasha Sergei Lavlov, za su tattauna kan batun Ukraine da Syria, da dangantakar dake tsakanin Amurka da Rasha a birnin Washington na Amurkan, a ranar 10 ga wata.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen ta bayar a jiya ta ce, bangarorin biyu za su tattauna kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya a gabashin kasar Ukraine, da aiwatar da yarjejeniyar Minsk wajen warware batun Ukraine a dukkan fannoni.

Game da batun Syria kuwa, ministocin za su tattauna kan yadda za a sassauta matsanancin yanayin da kasar ke ciki, da samar da gudummawar jin kai ga fararen hula, da shirya warware matsalar da take fuskanta a siyasance.

Yayin jawabin da ya yi a ma'aikatartasa ranar 3 ga wata, Tillerson ya ce babu amincewa da juna tsakanin Amurka da Rasha a halin yanzu, kuma dangantakar da ke tsakaninsu na cikin wani hali mafi tsanani tun lokacin cacar baki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China