in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kori jami'an kasar Rasha biyu daga kasarta
2016-07-09 13:25:42 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka John Kirby ya bayyana a jiya ranar 8 ga wata cewa, kasar Amurka ta kori jami'an kasar Rasha biyu daga kasar a ranar 17 ga watan Yuni don mayar da martani game da batun kai hari ga jami'in diplomasiyya na kasar Amurka a birnin Moscow na kasar Rasha.

Kirby ya sanar da wannan batu a gun taron manema labaru aka gudanar a wannan rana, amma ba tare da bada wani karin haske ba.

Kirby ya bayyana cewa, a ranar 6 ga watan Yuni, wani dan sandan kasar Rasha ya kai hari ga wani jami'in diplomasiyya na kasar Amurka wanda ya shaida mukaninsa yayin da yake shiga ofishin jakadancin Amurka dake kasar Rasha, wannan aiki ya kawo illa ga tsaron jami'in kasar Amurka.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Rasha suka bayar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mariya Zaxarova ta bayyana game da wannan batu cewa, bisa bidiyon da aka shaida, dan sandan kasar Rasha ya bukaci jami'in Amurka da ya shaida takardar ID don tabbatar da cewa ba zai kawo barazana ga ofishin jakadancin Amurka dake Rasha ba, amma jami'in ya kai hari gare shi. Amma Kirby ya ce, abin da bangaren Rasha ya fada ba gaskiya ba ne. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China