Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya yi maraba da irin ci gaban da ake samu, a dangantakar dake wanzuwa tsakanin kasashen Amurka da Rasha. Mr. Geng ya bayyana hakan ne a Juma'ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa.
Geng ya kara da cewa, kyakkyawar alaka tsakanin kasashe manya dake da kujerun dindindin a kwamitin tsaron MDD kamar Amurka da Rasha, zai taimaka wajen wanzar da tsaro da zaman lafiya a sassan duniya, tare da bada damar tinkarar kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta.
A cikin makon nan ne dai sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya kai ziyarar aiki kasar Rasha, inda sassan biyu suka bayyana ci gaba da ake samu, a dangantakar su cikin wadannan shekaru.(Saminu Alhassan)