John Kerry ya isa birnin Moscow ne a ranar 23 ga wata, domin fara ziyarar aiki karo na farko, bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Syria, bayan da kuma gwamnatin kasar Rasha ta sanar da janye sojojinta daga kasar ta Syria.
Haka kuma, dangane da batun Syria, Mr. Kerry ya bayyana cewa, kasashen Amurka da Rasha sun tsai da kudurin cewa, za su dukufa wajen ciyar da shawarwari kai tsaye a tsakanin tawagar wakilan gwamnatin kasar da 'yan adawar kasar gaba, domin aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD.
Kaza lika, za a kammala sauyin siyasa a kasar Syria, da kuma tsara daftarin tsarin mulkin kasar kafin karshen watan Agusta na bana. Kana kuma kasashen Amurka da Rasha za su ci gaba da karfafa tsarin tsagaita bude wuta a kasar Syria, yayin da kuma ake kawar da aikace-aikacen keta yarjejeniyar yadda ya kamata. Daga bisani kuma, kasashen biyu sun tabbatar da cewa, za a karfafa hadin gwiwa wajen warware matsalar Syria, a gabar da ake ci gaba da yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta IS. (Maryam)