Trump ya bayyana hakan a matsayin martini game da labaran da wasu kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka rika yadawa a 'yan kwanakin nan, suna zargin sa da bayyanawa kasar Rasha wasu sirrikan kasa.
Kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun bayar da labari cewa, a makon jiya, yayin da Trump yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, da jakadan Rasha dake kasar Amurka Sergey Kislyak, ya bayyanawa bangaren Rasha wasu sirri game da kungiyar IS.
Labarin ya bayyana cewa, sakon sirrin ya fito ne daga kasashen dake kawace tare da kasar Amurka, don haka wata kila hakan ya haifar da illa ga imanin da wasu kasashe suka yi da kasar Amurka.
Bayan da aka bayar da labarin, mai bada taimako ga shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa Herbert McMaster, ya bayyana cewa Trump da Lavrov, ba su tattauna kan sakon sirrin ko hanyar samun sakon sirrin ba, kana ba su tattauna duk wani aikin soja, da ba a fayyace a fili ba. (Zainab)