in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun nuna rashin amincewa da kudurin shugaban Amurka na mai da birnin Kudus, babban birnin Isra'ila
2017-12-08 11:05:29 cri
Ranar Laraba ne, kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta fara shirye-shiryen mayar da ofishin jakadancinta dake Tel Aviv zuwa birnin Kudus, bayan da shugaban kasar Donald Trump ya ayyana birnin na Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila a hukunce.

Dangane da wannan lamari, MDD, Masar, Burtaniya da wasu kasashen duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa suka nuna rashin amincewarsu da wannan kuduri na Amurka, sabo da a ganinsu, matakin zai kawo matsala a kokarin da ake na samar da zaman lafiya a yankin.

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, ba zai amince da duk wasu matakan da za su kawo cikas ga yanayin zaman lafiya a tsakanin Falesdinu da Isra'ila ba, manufar kasancewar kasashe biyu ce kadai za ta taimaka wajen warware matsalar yankin.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar, ta bayyana matakan da Donald Trump ya dauka na mai da birnin Kudus hedkwatar mulkin Isra'ila da cewa, ya saba da dokokin kasa da kasa, da ma kudurin MDD kan wannan batu. Kasar Masar na nuna damuwa sosai game da yanayin zaman lafiya a yankin.

Ita ma firaministar kasar Burtaniya Theresa May ta fidda sanarwar dake cewa, Burtaniya ba ta goyon bayan kudurin da kasar Amurka ta dauka, kuma kasar Burtaniya ba za ta canja ofishin jakadancinta daga Tel Aviv ba.

Haka zalika, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda wata sanarwa, inda ta yi allah wadai da kuduri na Amurka, tana mai cewa, hakan na iya bata ran al'ummomin Musulunmi, da kuma haddasa tashe-tashen hankula, har ma da rikice-rikice a kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China