Sanarwar da ma'akatar ta fitar a jiya, ta yi nuni da cewa, domin tabbatar da gudanar taron cikin nasara, kasar Togo tana bukatar gudanar da karin shirye-shirye. Sai dai kuma, sanarwar ba ta bayyana yaushe za a gudanar da taron ba.
Jaridar The Time of Israel ta ruwaito cewa, watakila za a soke gudanar da taron, la'akari da kin amincewa da shi da kasar Palesdinu da wasu kasashen Afirka su ka yi.
Don kyautata dangantakar dake tsakanin Isra'ila da kasashen Afirka, Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya taba kai ziyara kasashen Rwanda da Kenya da Uganda da Habasha da sauran wasu kasashen Afirka a shekarar 2016, kana ya halarci taron koli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar a kasar Liberia a watan Yunin bana. (Zainab)