in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da sake shigar da Koriya ta Arewa a jerin sunayen kasashe masu goyon bayan ta'addanci
2017-11-21 13:44:17 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Litinin cewa, an sake shigar da Koriya ta Arewa cikin jerin sunayen kasashen dake goyon bayan ta'addanci, tare kuma da kara mata matsin lamba. Manazarta sun bayyana cewa, kudurin zai iya tsananta sabanin dake tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Shugaba Trump ya sanar da wannan kuduri ne a taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a fadar shugaban kasar wato White House a wannan rana, kana ya bayyana cewa, ma'aikatar harkokin kudin kasar Amurka za ta kara daukar matakan kakabawa kasar Koriya ta Arewa takunkumi kan wannan batu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China