in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AL za ta yi taron gaggawa game da batun birnin Kudus
2017-12-06 20:44:50 cri

Kungiyar kasashen Larabawa ta AL, za ta gudanar da taron gaggawa na ministocin harkokin wajen ta a ranar Asabar din karshen mako, a wani mataki na tattauna halin da ake ciki, don gane da takaddamar da ta kunno kai bisa matsayin birnin Kudus.

Kamfanin dillancin labarai na MENA ya rawaito cewa, ana sa ran mahalarta taron za su yi musayar yawu, game da matakin da kungiyar za ta dauka, bisa muradin Amurka na maida birnin na Kudus hedkwatar mulkin kasar Isra'ila. Baya ga batun matsayin birnin bisa doka da tarihi, kamar dai yadda wata takardar jawabi ta gwamnatin al'ummar Falasdinawa ta ambata.

Taron dai ya biyo bayan bukatar hakan daga tsagin Faladinu ya gabatar, wadda kuma ta samu goyon baya daga kasar Jordan.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China