in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila na shirin gina sabbin gidaje 6000 a gabshin Kudus
2017-12-08 10:08:14 cri
Rahotanni daga Isra'ila na cewa, mahukuntan Isra'ilan na shirin gina sabbin matsugunan Yahudawa a birnin Kudus, ciki har da wasu gidaje 6,000 da gwamnatin ke shirin ginawa a gabashin birnin Kudus. Wannan mataki na zuwa ne bayan sanarwar da shugaba Doland Trump na kasar Amurka ya bayar game da ayyana birnin Kudus a matayin babban birnin Isra'ila.

Ministan harkokin gidaje da gine-gine na Isra'ila Yoav Galant shi ne ya gabatar da shirin gina gidajen, gami da wasu sabbi 14,000 da za a gina a yankunan daban-daban guda hudu na Isra'ilar.

Bayanai na nuna cewa, dukkan gidajen da za a gina sabbin ayyuka ne, ba sa cikin wadanda aka amince tun farko.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China