Trump ya ce, wannan mataki ya dace da muradun kasar Amurka da ma kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da al'ummar Palasdinawa.
Ya ce, mataki ne da tun bayan ba yau ba ya kamata a dauka, domin ciyar da shirin samar da zaman lafiya a tsakanin sassan biyu gaba. Sai dai kuma Trump ya musanta maganganun da bangarori da dama ke yi cewa, Amurka ta kauce daga shirinta na ganin an cimma yarjejeniya cikin lumana wadda bangarorin Isra'ila da na Palasdinwa za su amince da ita.(Ibrahim)