in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dubban matan Yahudawa da na Palastinawa ne suka yi maci a Jerusalem don lalibo matakan zaman lafiya
2017-10-09 10:33:08 cri
Dubun dubatar matan Yahudawa da na Palastinawa ne suka yi gangami a manyan titunan Jerusalem a ranar Lahadi domin yin kiraye kiraye neman a cimma matsaya don kulla yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

Wadanda suka shirya gangami sun yi kiyasin cewa, a kalla mata dubu 30 ne suka halarci taron wanda ya gudana a dandalin kwatar 'yanci na birnin Jerusalem.

Kungiyar mata mai rajin tabbatar da zaman lafiya wato "Women Wage Peace" ce ta shirya taron, kuma shi ne zagayen karshe na gangamin makonni biyu da kungiyar ta shirya wanda aka fara tun daga ranar 24 ga watan Satumba.

An fara gudanar da gangamin ne a kudancin birnin Sderot daga bisani ya bazu zuwa yamma da kogin Jordan.

An kafa kungiyar "Women Wage Peace" ne wajen shekaru 3 da suka gabata, don fafutukar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da kuma kawo karshen tashin hankalin dake sanadiyyar zubar da jini a tsakanin al'ummar Yahudawa da Palastinwa. Mambobin kungiyar kimanin dubu 24 suna bayyana aniyarsu na ci gaba da yin fafutukar har sai an cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China