in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsugunin Yahudawa yana kawo cikas ga shirin kafa kasashe biyu, in ji babban sakataren MDD
2017-08-30 10:42:26 cri
A jiya ne, babban sakataren MDD Antonio Guturres ya bayyana a birnin Ramallah cewa, yadda Isra'ila ke gina matsugunan Yahudawa yana hana ruwa gudu a kokarin da ake na aiwatar da shirin kafa kasashe biyu, shirin da ke da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila.

A wannan rana, babban sakataren ya yi shawarwari tare da firaministan Palasdinu Rami al-Hamdallah. A yayin taron manema labarai da aka kira bayan shawarwarin, Mr. Guterres ya jaddada cewa, MDD da shi kansa sun lashi takobin aiwatar da shirin kafa kasashen biyu daga dukkan fannoni. Ya ce, kamata ya yi shugabannin Palasdinu da Isra'ila su samar da yanayin da ya dace, kuma su dauki matakai na farfado da aminci da juna a maimakon nuna sabani, don gano bakin zaren warware matsalar da kuma kyautata zaman rayuwar Palasdinawa.

Mr. Rami al-Hamdallah a nasa bangaren ya ce, yadda gwamnatin Isra'ila ke kokarin gina matsugunan Yahudawa haka, na iya lalata shirin kafa kasashe biyu da ma damar da ke da ita ta wanzar da zaman lafiya a tsakanin sassan biyu. A cewarsa, Palasdinawa ba za su nade hannu suna zuba ido. A saboda haka, ya yi kira ga MDD da ta amsa kiran Palasdinawa na kare al'ummarta, tare da kalubalantar Isra'ila da ta aiwatar da kudurin da ya shafi batun Palasdinu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China