Mataimakin shugaban cibiyar Goddard ta hukumar harkokin sararin samaniya ta Amurka Li Can ya ce ya yi mamakin saurin raguwar adadin iskar ta Sulfur Dioxide da kasar Sin ta fitar, kuma bayanan nazarin da suka gabatar na nuna cewa, manufofin kiyaye muhalli da kasar Sin ta tsara sun taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Mr.Li ya nazarci bayanin da hukumar harkokin sararin samaniya ta Amurka ta fitar, wanda ya nuna cewa, a shekarar 2007, adadin iskar Sulfur Dioxide da kasar Sin ta fitar ya kai matsayin koli, wanda ya kai ton biliyan dubu 37. Sa'an nan, adadin ya ragu zuwa ton biliyan dubu 8 a shekarar 2016.
A kan fitar da iskar SO2 ne sakamakon kona kwal, wanda ya kasance babban dalilin da yake gurbata muhalli a kasar Sin. (Maryam)