Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Liu Yunshan, ya gana da 'yan tawagar ba da rahoto game da batun gandun daji na Saihanba a yau Laraba, inda a madadin shugaban kasar Xi Jinping, ya jinjinawa 'yan tawagar, da jami'ai, da ma'aikakan gandun dajin.
A yayin ganawar, Liu ya ce, mazauna gandun dajin Sai Hanba, na dagewa kan aikin dasa 'yayan itatuwa a cikin shekaru 55 da suka gabata, ta yadda suka kai ga mai da hamada zawa daji. Ya ce hakan ya zama abin koyi a fannin kiyaye muhallin halittu. (Bilkisu)