in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan Sin su gabatar wa kasa da kasa fasahohin kasar wajen kandagarki da magance kwararar hamada
2017-09-08 11:28:11 cri
A yayin taron fasahohin kasar Sin game da kandagarki da magance kwararar Hamada da aka yi a jiya Alhamis, a gefen babban taron mambobi, na kasashen da suka amince da shiga yarjejeniyar kandagarkin kwararar hamada na MDD karo na 13, wakilan kasar Sin sun gabatar da fasahohin kasar Sin a fannin.

Masanin cibiyar nazarin ilmin gandun daji na kasar Sin Lu Qi ya ce dalilan da suka sa aka sami sakamako mai kyau a kasar Sin a fannin kandagarki da magance kwararar Hamada shi ne, kyakkyawan jagorancin da gwamnatin kasar ta bayar, tare da goyon baya daga al'ummomin kasar, da ma fasahohi masu inganci da aka samu, da kuma dokokin kasar dake tabbatar da gudanarwar aikin yadda ya kamata.

Haka kuma, ya ce ana nazari kan fasahohin da suka jibanci wannan fanni, a matsayin wani muhimmin bangare na tabbatar da cimma nasarar gudanarwar ayyukan da aka sa gaba.

A nasa bangare, babban manaja na hukumar aikin kare gandun daji na kasar Sin Zhang Hongwen ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan raya fasahohi na kandagarki, da magance kwararar Hamada, inda ta sami sakamako da dama bisa fannonin daban daban da suka shafi haka. Kaza lika ta kuma gabatar da fasahohinta ga kasashen dake kan hanyar "Ziri daya da hanya daya", da mambobin kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da kasashen Afirka, da nufin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin.

A sa'i daya kuma, ta fara gudanar da hadin gwiwa da ofishin yarjejeniyar kandagarki, da magance kwararar hamada ta MDD, da kuma hukumar kiyaye muhalli na MDD, da wasu kungiyoyin kasa da kasa kan wannan aiki.

Bugu da kari, Zhang Hongwen ya ce, a nan gaba, kasar Sin za ta samar da horo kan fasahohin kandagarki, da magance kwararar hamada na kasa da kasa, domin samar da taimakon fasahohi ga kasashe da yankuna masu fama da wannan matsala. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China