Jami'ar wadda ta bayyana hakan yayin wata ziyarar kwanaki uku da ta kawo kasar Sin, ta kuma ce kasashe da dama na duniya sun rungumi wadannan matakai da kasar Sin ta yi amfani da su wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi a kasashensu.
Wasu daga cikin wadannan matakai da kasar ta Sin ta yi amfani da su, a cewar Madam Patricia, sun hada da fasahohin zamani marasa gurbata muhalli baya ga wasu sabbin dabaru duk da nufin inganta rayuwar Sinawa.
Jami'ar ta kuma bayyana mahukuntan kasar Sin, a matsayin jagorar magance matsalar sauyin yanayi a duniya. Ta ce kasar Sin ta aiwatar da managartan matakan alkinta muhalli a zahiri, wadanda suka samu yabo daga MDD. Har ma sun kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya.
Wannan dai ita ce ziyarar Madan Patricia Espinosa ta farko zuwa nan kasar Sin a matsayin jami'ar MDD mai kula da sauyin yanayi. (Ibrahim)