Cikin sanarwar bayan taron da aka fitar, an yabawa Gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayan da take bayarwa ga tsarin hadin gwiwar yaki da kwararar hamada karkashin shirin ziri daya da hanya daya, ta fuskar musayar ra'ayi kan fasahohi da karfafa kwarewar kasashen dake cikin kawancen.
Haka kuma taron ya bayayana aniyar kasa da kasa wajen yin hadin gwiwa kan yaki da kwararar hamada, da kuma amincewarsu ga shirin raya tattalin arziki a yankin hamada tare da kiyaye muhalli da kamar yadda aka aiwatar a Hamadar Kubuqi dake birnin Ordos na kasar Sin.
Babban taron mambobin kasashen da suka cimma yarjejeniyar yaki da kwararar hamada ta MDD karo na 13 da aka bude a ranar 12 ga watan nan da muke ciki, ya samu halartar wakilai sama da dubu 2, daga gwamnatocin kasashe 190 da suka cimma yarjejeniyar, da kuma kungiyoyin kasa da kasa sama da 20. (Maryam)