in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya halarci babban taron yarjejeniyar kare muhallin duniya
2017-09-20 13:57:38 cri
A jiya Talata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci babban taron yarjejeniyar kare muhalli ya duniya da aka yi a hedkwatar MDD dake birnin New York.

A jawabinsa yayin taron, Mr. Wang ya bayyana cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka kan ka'idoji guda hudu a yayin da muke inganta hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kiyaye muhallin duniya da kuma tsara yarjejeniyar kare muhallin duniya.

Wadannan ka'idoji guda hudu su ne, ya kamata a tattauna batun muhalli bisa jadawalin neman samun dauwamammen ci gaba, ta yadda za a cimma daidaito a tsakanin kiyaye muhallin duniya da raya tattaliln arziki da bunkasa zaman takewar al'umma.

Na biyu shi ne, ya kamata mu sauke nauyin dake wuyanmu yadda ya kamata kuma bisa yanayin da muke ciki, ta yadda za a taimakawa kasashe masu tasowa wajen neman dauwamammen ci gaba da kuma kiyaye muhallinsu.

Na uku kuma, ya kamata a amince da kiyaye 'yancin kasashen duniya kan albarkatun kasashensu, abu mai muhimmanci idan har da muna son habaka hadin gwiwar kasa da kasa a wannan aiki, kuma wannan shi ne, 'yanci da kundin tsarin MDD da dokokin kasa da kasa suka baiwa kasashen duniya.

Na hudu shi ne, ya kamata a sanya kasashe masu tasowa cikin aikin kiyaye muhallin duniya cikin himma da kwazo. Sabo da a yayin da suke kokarin neman bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'ummarsu, suna kuma da bukatar kiyaye muhalli a kasashensu, lamarin da ya sa, za su kasance wani muhimmin bangare cikin aikin kiyaye muhallin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China