Hukumar zabe mai zaman kan ta a Kenya ko IEBC a takaice, ita ce ta ayyana ranar 17 ga watan Oktoba mai zuwa, a matsayin ranar sake zaben shugaban kasar da aka soke. To sai dai Mr. Odinga ya bayyana cewa, hukumar ba ta yi musayar ra'ayi da tsagin NASA kan wannan rana ba.
Ya ce, ya kamata a dauki matakai domin tabbatar da gudanar babban zaben shugabancin kasar ta Kenya cikin yanayi na adalci, da biyayya ga tsarin mulkin kasar. Haka kuma, kamata ya yi a tattauna da bangarorin da abin ya shafa, game da yaushe ne za a sake zaben shugaban kasar, a maimakon kawai hukumar ta tsai da ranar da kanta.
A halin yanzu, dan takatar jam'iyyar Jubilee, wato shugaban mai ci Uhuru Kenyatta bai bayyana ra'ayinsa kan ranar sake zaben da hukumar IEBC ta fidda a jiya ba. (Maryam)