Shugaban kasar Kenya mai ci Uhuru Kenyatta ne dai aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben. To sai dai kotun kolin ta ce sakamakon da aka fitar cike yake da magudi.
Al'ummar Kenya dai sun yi dakon hukuncin kotun a 'yan kwanakin nan, tun bayan da tsagin gamayyar 'yan adawar kasar NASA wadda Raila Odinga ya yiwa takara, ya sha alwashin kalubalantar sakamakon da aka fitar.
Mr. Odinga dai ya gabatar da korafin sa na kalubalantar wannan sakamako, ciki hadda wasu shaidu dake nuna yadda aka yi aringizon kuri'u, da kutse cikin na'urorin tattara sakamakon zaben, da kuma yadda aka yi amfani da kudaden gwamnati wajen yakin neman zaben shugaban kasar mai ci.
Alkalai hudu ne dai suka goyi bayan shaidun Mr. Odinga, yayin da sauran biyu kuma suka ki amincewa da shaidun. Masana shari'a dai na ganin hukuncin kotun kolin ta Kenya, ya shiga kundin tarihi, kasancewar sa na farko a Kenya, ba kuma safai ake ganin irin sa a nahiyar Afirka ba.