in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na goyo bayan amfani da ababen zuba kaya sabanin leda
2017-08-25 10:30:54 cri
Mahukunta a kasar Kenya, sun fidda wani sabon tsarin karfafawa al'ummar kasar gwiwa, wajen amfani da wasu ababen zuba kayayyaki da suka sha banban da leda, gabanin aiwatar da sabuwar dokar haramta amfani da leda baki daya a fadin kasar.

Babbar jami'i dake kula da harkar kula da muhalli a kasar Judi Wakhungu ce ta tabbatar da daukar wannan mataki, bayan da wata kotun kasar ta dakatar da aiwatar da dokar haramta amfani da ledar.

Wakhungu ta ce amfani da sabbin nau'oin ababen zuba kaya da suka sabawa leda, zai taimaka wajen kiyaye muhalli, da samar da ayyukan yi a fannin sarrafa bola, tare da kyautata tsarin kiwon lafiyar al'umma, da kare muhallin halittu. Jami'ar ta bayyana hakan ne a birnin Nairobi yayin wani taro na baje kolin nau'oin ababen zuba kaya da suka dace da yanayin kare muhalli.

A farkon watan nan ne dai gwamnatin kasar ta ayyana ranar 28 ga watan nan, a matsayin ranar fara aiwatar da dokar haramta amfani da leda, saboda irin tasirin ta ga gurbatar muhalli. To sai dai kuma wasu kamfanonin sarrafa leda a kasar sun kalubalanci hakan gaban kuliya, suna masu cewa hakan zai toshe kafofin ayyukan yi, da ma rage haraji da gwamnati ke samu daga sarrafa ledar.

Bisa hakan ne kuma alkalan kotun suka bada umarnin dage wa'adin fara amfani da wannan doka ta gwamnatin Kenya har sai bayan watanni 6 masu zuwa, domin baiwa irin wadannan kamfanoni damar rabuwa da tarin ledar da suka riga suka sarrafa. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China