Haka kuma, ya yi kira ga al'ummomin kasar da su kwantar da hankulansu domin kiyaye zaman lafiyar yadda ya kamata.
A ranar 11 ga watan Agustan da ya gabata ne, hukumar zabe ta kasar Kenya, ta sanar da sakamakon babban zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 8 ga watan na Agusta, inda ya bayyana shugaban mai ci Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya sake lashe zaben, bisa samun kaso 54.27 bisa dari na kuri'un da aka kada.
Sai dai dan takatar jam'iyyar adawa ta kasar NASA wato Raila Odinga, ya ki amincewa da wancan sakamako, inda ya kalubalance shi a gaban kotun kolin kasar.
A kuma jiya Juma'a ne, kotun kolin kasar ta Kenya, ta sanar da soke sakamakon zaben da aka yi a watan da ya gabata tare da ayyana shi a matsayin wanda bai yuwu ba, inda ta bukaci a sake gudanar da babban zaben cikin kwanaki 60 masu zuwa.
Rahotanni na cewa, hukuncin da kotun kolin ta yanke ya jefa damuwa a zukatan mutane dangane da yanayin siyasar kasar ta Kenya. (Maryam)