in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta kaddamar da amfani da na'urorin binciken kayayyaki da kasar Sin ta taimaka mata da su
2017-08-26 12:46:38 cri

An kaddamar da na'urorin binciken kayayyaki guda 3, da kasar Sin ta taimakawa Kenya da su, jiya Jumma'a a tashar jiragen ruwa dake Mombasa.

Da yake jawabi yayin bikin kadaddamarwar, kwamishinan hukumar tattara kudaden shiga na kasar John Njiraini, ya ce sabbin na'urorin sun kunshi biyu da ake kafawa, da kuma guda da ta kasance tafi da gidanka, yana mai cewa za su inganta ayyukan hukumar na binciken dukkan kayayyaki domin kawar da hadari.

Ya ce yanzu haka, suna amfani da sabbin na'urorin wajen binciken kimanin kwantenonin kaya 500 a ko wacce rana, kuma suna sa ran adadin ya karu zuwa kimanin 750 kwatankwacin kashi 30 cikin dari na dukkan kayayyaki. John Njiraini ya waiwayi ziyararsa a tashar jiragen ruwa ta Shanghai na kasar Sin, inda ya ga yadda ake amfani da fasahar zamani wajen saukaka ayyukan kwastam.

Ya ce babu mutane a babbar tashar kuma ana gudanar da ayyukan ne kai tsaye da na'urori, yana mai cewa Kenya za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin domin amfana da fasahohin binciken kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China