Odinga, ya shedawa taron 'yan jaridu a Nairobi cewa, zai kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar wanda aka bayyana shi a ranar Jumma'ar da ta gabata a gaban babbar kotun kasar, sakamakon zaben dai ya nuna cewa, mista Uhuru Kenyatta shi ne ya yi nasara a zaben.
Idan za'a iya tunawa a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2013, kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da madugun 'yan adawar kasar ya shigar a gabanta, bayan ta hukumar zaben kasar Kenyan ta sanar da Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben, kotun ta yi ikirarin rashin samun gamsassun hujjoji daga bangaren wanda ke karar.
Odinga wanda ya fadi a zaben shugaban kasar har karo na 3 a lokutan baya, ya tabbatar da cewa, zai gabatarwa kotun kwararan hujjoji dake tabbatar da cewa an tafka magudi a zaben, bayan da aka bayyana shugaba Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben. (Ahmad Fagam)