in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsai da ranar sake zaben Kenya
2017-09-05 08:49:27 cri

Hukumar zabe mai zaman kan ta a kasar Kenya IEBC, ta ayyana ranar 17 ga watan Oktoba mai zuwa, a matsayin ranar sake zaben shugaban kasa, bayan da kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 8 ga watan Agustar da ya gabata.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban hukumar zaben ta IEBC Wafula Chebukati, ya ce manyan 'yan takara biyu a zaben, wato shugaban mai ci Uhuru Kenyatta da mataimakin sa William Ruto, tare da dan takarar bangaren 'yan adawa Raila Odinga da mataimakin sa na takara Kalonzo Musyoka ne kadai za su fafata a zaben na tsakiyar wata mai zuwa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai kotun kolin kasar ta Kenya, ta rushe zaben da aka gudanar, wanda ya baiwa shugaba Kenyatta nasara, tana mai cewa, zaben ba shi da inganci, domin kuwa an tafka magudi da karya dokokin kasa a cikin sa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China